FITILAR RAYUWA:
Ko shakka babu wayoyin celulla a zamanin nan da muke ciki ya zama tamkar ruwan dare wajen amfanin yau da kullum dan ya zamana gasa a tsakanin al’umma, shin ya mutane suka dauki waya da muhimmanci, shin ko wacce irin rawa waya ke takawa a wannan zamani.
Jama’a assalamu alaikum,
barkan mu da kara kasancewa da ku ta cikin sabon shirin.
Ita dai wannan duniya
da mu ke ciki a wannan karni da muke, ta zo da sauye-sauye kala daban-daban;
hakan ya kawo abuwawa da dama wanda suka zaman hatsi leka gida kowa domin a
yanzu wayoyin hannun sun zama gama-gari, domin gidan kowa idan kaje akwai waya
duba da yanayin zamani da ya juya shine a turance ake cewa globalization.
Waya dai wata abace
wacce ta zaman kamar wani bangare na rayuwar wasu al’umma wanda idan babu ita, ba
sa iya rayuwa. Ko kuwa idan wayar su ta samu matsala ji su ke tamkar wani
babban gurbin na rayuwarsu ya durkushe.
Haka yasa masana da
dama, da ma mutane da yawa ke furucin cewa waya ta zaman wani babban jigon na rayuwar
mutane na yau da kullum.
Kamar yadda kowa ya sani,
ita dai waya ana amfanin da ita ne ta bangarorin daban daban kamar wajen sada zumunci ciki sauki, kuma wata hanya ce
mafi sauki da za ta fadakar, ta kuma illimantar da al’umma kuma tana iya gurbata
tarbiyya ko ta gyara; amman mafi akasari tafi zaman silar gurbartar tarbiyya.
Hakan yasa wasu ke ma
waya fassara daban-daban, wasu kuma iyayen ke hana ‘yayan su rike waya a
hannunsu ko kuma hana su layin waya, wanda shima layin na taka muhimmiyar rawa
a waya.
Wasu na ganin kamar wayewa ne mutum yayi sa’oi ashirin da hudu na ranakun mako yana amfani da wayar hannu.
A kokarin mu na hawa kan
tsauni da muke kokarin dubawa na muhimmanci amfani da waya a bangaren mata,
wasu na hangar illolin sa da kuma muhimmiyar rawa da wayar ke bayarwa ga
al’umma. Wai shin dagaske ita waya tana da amfanin a rayuwar al’umma ta yau da
kullum? Wane irin kallo al’umma suke yi wa waya?
Shi a wannan karnin da
muke ciki akwai bambanci tsakanin dattijo mai amfanin da waya ko matashi?
Iyayen mu mata da masu aure shin ya suke kallon waya a nasu bangaren? Kuma ya
suke amfanin da ita?
Duk wadanan tambayoyi na
zuwan ne bayan wasu masana sun nazarci abubuwa da ke faruwa a wayoyin tafi da
gida ka wace aka fi sani da cellula, musamman ta bangaren mata wanda sanadiyar
haka ke sa wasu ke samun sabani da abokan zaman su ko kuma mazajensu wanda haka
zai iya haifar da mace-macen aure wanda ya zaman matsala ga al’ummar arewanci Najeriya.
A yanzu dai waya ta
zama gasa a tsakanin wasu daga ciki y’an
mata, zawarawa harma da matan aure domin wata kanyi komai domin ta mallaki waya,
wata kuwa ta kan iya sabawa ubangijin ta domin rike waya ko da mijinta bashi da
halin siya mata, sai tayi yadda tayi ta mallaki waya ko da kuwa mijin nata baya
so.
Su dai mata mafi aksari
tsegumin ne ke kaisu ga amfanin da waya, wata kuwa chat, take da saurayi ta
bayan cewa a mata baiko, a bangaren matan aure kuwa abin ba kyan ganin, dan za kaga
mace mai aure tana turawa wani bare hotunan ta, ko tayi chat din bandala tare
da wani daban, wanda hakanne ke janyo ta fada a hallaka daga karshe kuma idan
assirin ta ya tonu mijin ta ya saketa ta rasa madogarar dafawa.
Ita dai waya inuwar
bangaruwa ce ga mai kaya ga sanyi, zamani fah riga ce to ba fah ko wace rigar
bace zaka yafa ta maka kyau wata idan kasa bai zama lalle ta miki kyau ba,
domin zaiyi kamar kin sanya wani kayan mahaukaci ne, ko wata kaga ya mata
daidai ko kuma na wata ya na jan kasa.
Ita dai zuciya itace
mutum kuma ta ka iya raiya masa komai alokaci da ta rufe masa ido, minddin zuciya ta gurbata mutum ya illata kenan.
kuma da zarar ta karye bazata dauru ba kamar yadda ake iya daura mutum a kafa
ko a hannu, sannan zuciya idan abu bako ya zo a gareta a karon farko ta kan kyamace shi kafin ta amince
dashi. Daga bisani kuma ta kwakwayi abin domin birgeta da yayi wanda banza tayi
duba da cewa mai kyau ne ko ba mai kyau bane.
Waya dai ta bata auren
da bashi da adadi, kuma ta ruguza zaman lafiya tsakanin masoya bila adadin kana
ta kuma ruguza aura da ana dab da daurawa wanda banzai misaltu ba, ta kuma
ruguza baikon da banzai lissafu ba, sabo da rudin duniya.
Akawai dai tufka gami
da warwara da masana da ma al’umma keyi wajen ganin su rage, ko su daidaita
abubuwa dake faruwa dan gane da wayar cellula a hannun mata amman hakan dai
kamar da wuya domin idan a gyara tabbas akwai wandada suke batawa kuma su rufe.
Kawaye ma na taka
muhimiyar rawa a wannan fanin idan ake samu wasu kawayen da suka fi uwar miji
da dangi da kuma saurayi da aka muku baiko.
Wasu yan matan kamar yadda akayi hassahen kwadayi da son abin
duniya ne kekai su da amfanin da waya ta gurbataciyar hanya; wasu kuwa domin su
birge ne, wasu kuma domin uzirinsu ne kamar sana’a da sauransu.
Haka yasa muka waiwayi Dr. Mu’azu Kudan na jami’ar sule lamido dake Kafin Hausa anan jihar jigawa domin yamana mana sharhin akan amfanin da wayar cellular da ake addabar matan aure, yan mata da zawarawA...
Kamar yadda Dr. Kudan
ya fadi cewa ka shuka abu mai kyau ka girba anan gaba domin neman irin ka, koda
baka doron duniya.
Wai shin maiyasa
matayan aure ba zasu iya hakura ba, sai ta nuna cewa ita ta isa takai wani matsayi,
ma’ana tana da class (aji). Irin wannan class din ne a bangare guda yake
rijayar wayansu matan musamman ta bangaren anko, domin neman aji da sutura.
Yan ga waya, ku sanin
fah sutura bashi bane ke nuna kina da kudi ko kuma kin kai matsayin ayi
kwatacce dake ba, domin idan muka waiwaye asalin anko shi karan kansa ya sabawa
al’adun mu. Kuma idan muka hanga za muga wannan rayuwar ta anko aronta mukayi a
gurin wasu al’umma na daban.
Kamar yadda yake ba
ibada bane ayi anko, kamar yadda sallah
take ibada ba, bai kamata ace yan mata suna kashe kudadensu ba, indai bai zama dole ba. Idan za zamu ga idan
ma ba ayi anko ba wani har gaba zai nayi dake domin a cewarta, ita tayi naki ke
kuma baki yi nata ba haka sai ya janyo gaba a tsakanin ku ko sa’insa... Wai shin
mai yasa baza muyi duba da yanayi almobazarancin da muke yi?
Ba kuma duk mace ba ce
za’a mata kitso ya mata kyau kuma ya sako har kafadarta ba, face ta kara zaren
kitso a gashi ta.
Dr. Kudan yayi karin bayani
dangane da yadda anko ya samo asali a kasar Hausa da kuma yadda ya sabawa
al’adun mu.
Wai mai yasa baza muyi amfanin da kudin anko domin gina wani gurbin na rayuwar bamu ba. Kice dole sai kinsa anko ko kin rike waya mai tsada domin cinyewa ba. Idan kina son cinyewa ya kasance kina da tsari da tanadi wanda za kiyi amfani dashi, ba sai kincewa saurayi ko mijin ki, ko iyayenki su baki ba. Domin koda su iyayen naki ne idan yau suka baki to gobe idan kika dawo bai zamana ace su sake baki ba. Dan haka ki tashi ki nemi naki karkii bi kyale-kyale zamanin nan domin watarana zaki rike fiye da irin wannan a rayuwa.
Yatsun mu ba daya suka
taru suka zama daya ba, wani ya fi wani girma. Rayuwa tanada sauki idan har
mutum ya tsaya yayi abin da ya kawoshi kafin lokacin da zai koma ga mahalicin
sa, yana mai farinciki da babban tagomashi da zai samu acan sakamakon aikin
alkairi daya aikata a doron duniya. Mutum ya tsaya a iya inda Allah ya ajiye
shi. Kuma irin wannan hange-hangen na kawar ku, ko kuwa yar ajinku, ko kuma
makociyar ku, ko kuma yar unguwa ku, shi zai kai ki fada ga babban hallaka.
Lokaci wucewa yake sannan
abubuwan zamani kara bayana suke mai zai hana muyi amfani da dan karamin lokacin
da muke dashi a rayuwa ba domin gina abin da za’ayi alfahari damu, ko kuma mu
zamana abin kwatance koda bayan ran mune ace wace ce ana neman irinta.
Tabbas baza mu iya rayuwa babu waya ba, sannan kuma babu sutura ba. Kiyi safan-saffan ba tare da takura ba sannan kuma ki rike darajar auren ki da martabar ki, domin ita mace Allah ya mata lokaci kalilan. Saboda haka, wannan lokacin kiyi kokarin yin amfani dashi ta hanya mafi sauki da bazai janyo miki dana sani ba a rayuwa.
To jama’a, duka-duka
anan muka kawo karshe shirin na mu. A madadin Dr. Kudan da kuma jagoran shirin,
Babangida Usman Hdj sai ni da na sirya na gabatar Sodikat Umar Meamalari nake
cewa saduwar alkhairi.
Hakkin Mallaki:
Sodikat Umar Meamalari
Sodikataishamar0150@gmail.com
0 Comments